top of page
  • Artv News

Majalisar karamar hukumar Gwarzo ta rage mukamin wani dan siyasaMajalisar Karamar hukumar Gwarzo ta sanar da rage matsayin babban mataimaki na musamman ga shugan Karamar hukumar Umar Hamza Zakari daga kan mukaminsa nan take.


Da yake sanar da wannan matsayin kwamitin bincike da aka kafa karkashin shugabancin kakakin majalisar Karamar hukumar Auwalu sani Lakwaya ya samu Umar Hamza Zakari da laifi dumu dumu Wanda ya kunshi laifin karya kaidoji gudanar da aiki.


A sanarwar da jami'in yada labarai na shiyyar Gwarzo, Rabi'u Khalil ya fitar, ta ce Kwamitin ya rage matsayin Umar Hamza Zakari daga babban mataimaki namusamman na daya zuwa mataimaki na musamman na biyu.


Auwalu Sani Lakwaya ya shawarci masu rike mukamai a majalisar Karamar hukumar dasu rinka gudanarda aikinsu cikin gaskiya da rikon Amana.


A kokarin jin tabakin Umar Hamza Zakari yaci tura lokacin hada wannan sako.

Anasa jawabin sakataren kwamitin Daraktan mulki na Karamar hukumar Ibrahim Alkassim Wanda ya Sami wakilcin shugaban sashen ayyuka na musamman ya shawarci maaikatan Karamar hukumar dasu zage damtse da daina wasa da aiki domin majalisar Karamar ta daina lamuntar sakaci da lalaci.


A wani cigaban kuma shugaban majalisar Karamar hukumar Gwarzo ya yabawa gwamna Dr.Abdullahi Umar Ganduje bisa Mika sunan Ibrahim Danazumi Gwarzo ga majalisar dokoki ta jiha don tantaceshi a matsayin kwamishina.


Bashir Abdullahi Kutama yace zaa ajiye kwarya a gurbinta domin gogewarsa a fannonin daban daban days kunshi siyasa da harkokin gwamnati da kasuwanci.


48 views0 comments
bottom of page