top of page
  • Writer's pictureArtv News

Macron ya gaza samun rinjaye a zaben majalisar dokokin Faransa


Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gaza samun rinjayen da ya ke bukata a majalisar dokokin kasar bayan gagarumar nasarar da sabuwar hadaka ta masu sassaucin ra’ayi da masu tsatsauran ra’ayi suka samu a zaben ‘yan majalisar dokoki na jiya Lahadi, abin da ya kasance babban koma-baya ga shirin shugaban na kawo sauye sauye a wa’adi na biyu da ya samu kwanan nan.

Sakamakon zaben na ranar Lahadi ya jefa siyasar Faransa a cikin rudani, lamarin da ke ta’azzara yiwuwar samun majalisar dokoki mara karsashi, ko kuma hadaka mara inganci da tasiri, duba da yadda ya zame wa Macron tilas ya nemi goyon bayan sabuwar hadaka da ta kada shi.

RFI ta rawaito cewa, yanzu Macron, mai shekaru 44 yana fuskantar barazanar yin tsamotsamo a cikin matsalolin ciki gida, a daidai lokacin da yake neman kasancewa a kan gaba wajen kawo karshen mamayar da Rasha ta ke yi wa Ukraine, tare da ci gaba da zama mai fada- a- ji a Tarayyar Turai.

Hadakar shugaba Macron ta ‘Ensemble’ ce dai za ta ci gaba da zama jam’iya mafi girma a majalisar dokoki mai zuwa, amma da kujeru 245, kamar yadda sakamakon zaben da ma’aikatar cikin gidan kasar ya nuna a safiyar Litinin din nan, abin da ke nuni da cewa ta gaza samun kujeru 289 da take bukata ta samu rinjaye a majalisar mai kujeru 577.

Yanzu haka dai mukarraban shugaba Macron sun sha alwashin aiki tukuru don bijiro da hadakar da za ta basu rinjaye a majalisar dokokin kasar, kamar yadda Fira minista Elizabeth Borne ta bayyana a wani jawabi da aka watsa ta talabijin.

6 views0 comments
bottom of page