top of page
  • Writer's pictureArtv News

Liverpool ta kammala daukar Fabio Carvalho daga Fulham, wanda ake sa ran dan wasan zai koma Anfield
Mai shekara 19 ya taka rawar gani da ta kai Fulham ta samu tikitin shiga Premier League a badi, bayan cin kwallo 10 da bayar da takwas aka zura a raga a bana.

Tun farko kungiyoyin biyu sun cimma yarjejeniya ta daukar dan kwallon a watan Janairu, daga baya batun ya bi ruwa.


Carvalho ya buga wa tawagar kwallon kafa ta matasan Ingila 'yan kasa da shekara 21 tamaula, wanda ya fara yin wasan farko da Portugal a watan Maris.

Ya fara tamaula daga matasan Fulham, wanda ya yi takarar gwarzon dan wasan English Football League, inda Brennan Johnson na Nottingham Forest ya lashe kyautar.

Ranar 28 Liverpool za ta buga wasan karshe da Real Madrid a gasar Champions League a Faransa.


Liverpool na fatan daukar kofin Zakarun Turai na bakwai, ita kuwa Real Madrid na sa ran cin na 14 jumulla.


Liverpool wadda ke fatan lashe kofi hudu a bana ta rasa Premier League a ranar Lahadi, bayan da Manchester City ta dauki na shida jumulla.


Kungiyar Anfield ta yi nasarar daukar Caraboa Cup da FA Cup a bana, wanda ta doke Chelsea ta kuma lashe kofunan a kakar nan.


8 views0 comments
bottom of page