Artv News
LABARI DA DUMIDUMINSA: Gwamna Ganduje ya sauya sunan Jami'ar kimiyya da fasaha ta Wudil

Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta amince da sauya sunan Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano dake Wudil KUST da Sunan Aliko Dangote
Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce ci gaban ya biyo bayan shawarar da kwamitin da aka tura jami’ar ya bayar.

Ya bayyana cewa a yanzu za’a rika kiran makarantar da suna Aliko Dangote University of Science and Technology (ADUST), Wudil.
Malam Garba ya kara da cewa an mika batun ga majalisar dokokin jihar domin nazarin dokokin da suka kafa jami’ar domin yin gyara.