Artv News
Kwamitin tantance yan takarar Shugaban kasa a APC ya cire mutane 10 cikin 23
Shugaban Kwamitin tantance yan takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar APC Cif John Odigie-Oyegun ya cire mutane 10 daga cikin 23 da suka nemi takarar shugaban kasa a jam’iyyar, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Ko da yake ba a kai ga bayyana jerin sunayen wadanda abin ya shafa ba, a halin yanzu kwamitin yana sakatariyar jam’iyyar ta kasa domin mika rahoton sa ga kwamitin kolin jam’iyyar wanda ke karkashin Sanata Abdullahi Adamu.
Majiyarmu ta rawaito dama dai ana ta kokawa Kan kin bayyanawa al’umma Sakamakon aikin da Kwamitin yayi, kasancewar baifi kwanaki suka rage a shiga zaben fidda gwani na kujerar Shugaban kasa a Jam’iyyar ba.
Cikakken labarin na nan tafe
