top of page
  • Writer's pictureArtv News

Kotun ECOWAS Za Ta Yanke Hukunci Kan Zaben Shugaban Kasar Nijar

A yau [Talata] ce ake sa ran kotun Kungiyar Cinikayyar Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) za ta yanke hukunci kan karar da kalubalantar nasarar da Bazoum Muhammad ya samu a zaben Shugaban Jamhuriyar Nijar na 2021.


Daya daga cikin ’yan takarar da suka fafata a zaben, Mahamane Ousmane, ne ya shigar da karar a gaban kotu yana kalubalantar gwamnati da take hakkin dan-Adam a zaben Shugaban Kasar.


Jaridar Aminiya ta rawaito cewa Bazoum dai ya samu nasara a zaben ne da kaso 55.75 cikin 100 na kuri’un da aka kada, sai kuma Mahamane Ousmane da ke ya samu kaso 44.25.


Hakan ne ya sanya shi garzayawa kotun ECOWAS bayan Babbar Kotun Jamhuriyar ta Nijar ta sanar da soke zabukan cibiyoyin zabe 75 ba tare da bayyana dalilanta ba, kamar dai yadda gidan talabijin na Aljazeera ya rawaito.


Ousmane dai bai amince da zaben ba ne domin a cewarsa, ya saba wa dokoki da Kundin tsyarin Mulkin kasar.


Kazalika, ya ce akwai yunkurin dakile samun nasararsa a karo na biyu ranar 21 ga watan Fabrairu da aka gudanar da zaben, saboda kin duba kokensa da Kotun Tsarin Mulkin kasar ta yi.


Don haka ne ya daukaka kara zuwa kotun ECOWAS, yana kalubalantar hukuncin kotun baya ta yanke na inganta zaben Bazoum a matsayin zababben Shugaban Nijar.


Idan har kotun a yau ta gamsu da hujjojin tsohon dan takarar, hakan zai zamo ta leko ta koma ga mulkin Bazoum, kuma akwai yiwuwar Ousmane ya koma Shugabancin Nijar din.

9 views0 comments
bottom of page