top of page
  • Writer's pictureArtv News

Kotun Amurka ta aike da mawaki R. Kelly gidan yari na shekaru 30


Wata Kotu a Amurka ta yankewa fitaccen mawakin kasar R. Kelly hukuncin daurin shekaru 30 a gidan yari, saboda samun sa da laifin kwashe shekaru ya na yaudarar mata da 'yammata domin lalata da su.

Mai shari’a Ann Donnelly ta zartar da wannan hukunci a kotun tarayya da ke Brooklyn kusan shekara guda bayan samun fitaccen mawakin da aikata laifi a New York.


RFI ta rawaito cewa R. Kelly na daga cikin fitattun mawakan Amurka na R&B da suka yi fice a duniya kafin daga bisani ya samu kan sa wajen aikata aika aikar wadda ta kaiga yanke masa wannan hukuncin.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun mawaki a Amurka da wannan dabi'a ba sai dai hukuncin shi ne irinsa na baya-bayan nan da kotu ta zartas.

36 views0 comments
bottom of page