top of page
  • Writer's pictureArtv News

Kotu a Najeriya ta umarci malaman jami'o'in kasar su janye yajin aiki


Kotun ma’aikata da ke Abuja ta umarci kungiyar malaman jami’o’in kasar, da ta janye yajin aikin da take yi.

Mai shari’a Polycarp Hamman ta ce yajin aikin ya saba wa sashe na 18 (1) (2) na dokar aiki, wanda ya haramta yajin aikin nasu. Hamman ta bayyana cewa yajin aikin ya haifar da barnar da ba za a iya misalta ba ga rayuwar dalibai da dama a Najeriya.

Mai shari’a Hamman ta mika karar zuwa ga shugaban kotun domin a sake masa mukami. A ranar 14 ga Fabrairu, 2022, ASUU ta tsunduma yajin aikin neman a sake tattaunawa kan yarjejeniyar da suka kulla da gwamnati a 2009, da dai sauransu.

Tattaunawar da aka yi tsakanin ASUU da gwamnati ba ta haifar da sakamako ba, abin da ya sanya daga bisani gwamnatin Najeriya maka ASUU gaban kotu.


(RFI)

8 views0 comments
bottom of page