top of page
  • Writer's pictureArtv News

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Mane, Salah, Bale, de Jong, Kounde, Matthijs da Botman
Tottenham ba ta da niyyar siyan kyaftin din Wales Gareth Bale a karo na uku yayin da dan wasan mai shekara 32 ke tunanin yaddazai shirya wa gasar cin kofin duniya ta bana.


Dan wasan gaban Senegal Sadio Mane, mai shekara 30, ya tambayi abokin wasan Liverpool kuma tsohon dan wasan Bayern Munich Thiago Alcantara ko zai iya shiga gidansa da ke Munich idan ya koma kungiyar ta Bundesliga a bana.


Barcelona na shirin tattaunawa da Manchester United kan batun dauko dan wasan tsakiyarta na Netherlands Frenkie de Jong, mai shekara 25, zuwa Old Trafford amma har yanzu kulob din na Sifaniya bai samu tayi a hukumance daga United ba.


Chelsea na zawarcin dan wasan baya na Juventus dan kasar Holland Matthis de Ligt, mai shekara 22, amma ga kocin Blues din Thomas Tuchel, babban abin da ke gabansa shine dauko dan wasan bayan Sevilla mai shekara 23 Jules Kounde.


Dan wasan baya na kasar Holland Sven Botman, mai shekara 22, wanda ake alakanta shi da komawa Newcastle, ya ce har yanzu AC Milan na kokarin kammala cinikinsa daga Lille.


Rahotanni sun ce dan wasan baya na Ingila James Tomkins, mai shekara 33, ya rattaba hannu kan sabon kwantiragi na shekara guda da Crystal Palace, yayin da dan wasan tsakiyar Scotland James McArthur, mai shekara 34, shi ma ya amince da sabon kwantaragi a Selhurst Park.

BBC Hausa

16 views0 comments
bottom of page