top of page
  • Writer's pictureArtv News

KAROTA ta kama mota makare da Giya a Kano


Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) ta ce ta sami nasarar cafke wata tirela makare da giya a kan titin Bello Dandago da ke kwaryar birnin Kano.


Jami’an na KAROTA sun kama motar ne da misalin karfe 2:30 na daren Larabar da ta gabata, lokacin da take kokarin shiga unguwar Sabon Gari.


Jami’an sun cafke motar ne a lokacin da suka bukaci direban motar ya gabatar musu da takardar shaidar kayan da ya dauko, inda ya bayyana musu cewa kwali ne a cikin motar.


Sai dai bayan da jami’an suka matsa bincike, sai suka tabbatar da giya ce a cikin motar.

Shugaban hukumar ta KAROTA, Baffa Babba Dan-Agundi, ya ce ba za su gajiya ba wajen kama duk wani nau’in kayan da aka ci garo da su, wanda dokar jihar ba ta amince a shigo da su ba.


Ya kuma ce za a kara baza jami’ansu musamman kan manyan titunan jihar domin ganin an dakile shigowar kayayyakin da dokar jihar Kano ta haramta.


A cikin kasa da mako guda dai, hukumar ta cafke manyan motocin Tirela makare da Giya wadanda adadinsu ya kai fiye da kwalba 40,000, wacce kudinta ya haura Naira miliyan 40.


Ya ce zarar sun kammala bincike za su mika ta ga hukumar Hizba ta jihar domin daukar mataki na gaba.


5 views0 comments
bottom of page