Artv News
Juventus ta dauki Gleison Bremer daga Torino

Juventus ta kammala daukar mai tsaron bayan Brazil, Gleison Bremer daga abokiyar hamayya Torino.
Dan wasan ya amince da kunshin yarjejeniyar kaka biyar a kungiyar ta birnin Turin kan fam miliyan 34.8.
Mai shekara 25 ya maye gurbin dan kwallon tawagar Netherlands, Matthijs de Ligt, wanda ya koma Bayern Munich ranar Talata.
Bremer ya yi wa Torino wasa 110 tun bayan da ya koma Italia da taka leda daga kungiyar Brazil, Atletico Mineiro a 2018.
Ya buga karawa 33 daga 38 a Serie A kakar da ta wuce, shi ne aka zaba a matakin mai tsaron baya da ba kamarsa a babbar gasar tamaula ta Italiya a kakar 2021-22.