top of page
  • Artv News

Jami’ar da ta fi kowacce a Najeriya ce ta 400 a duniya


Cibiyar nan da ke fid da matsayin jami’o’i a duniya wato The Times Higher Education World Rankings ta ayyana jami’ar Afe Babalola da ke Jihar Ekiti a matsayin wacce ta fi kowacce a Najeriya, kuma ta 400 a duniya.


Jaridar Aminiya ta rawaito cewa, Shugaba Buhari ya taya Shugaban jami’ar da ma’aikanta murnar zamowa jami’ar da ta fi kowacce a Najeriya.


Haka zalika Buhari, a sakon taya murnar da ya fitar ta bakin kakakinsa Femi Adesina ranar Litinin, ya yaba wa tsare-tsaren jami’ar, da ya ce sune suka kai ta ga wannan matakin.


Ya kuma ce zamowa zakaran gwajin dafi daga jami’o’i 197 da ke Najeriya, da kuma kasancewa ta 400 a duniya daga cikin 31,097, ba karamar nasara ba ce ga Najeriya baki daya.


Don haka ya taya shugabanni da ma’aikatan jami’ar murna, tare da fatan za su cigaba da jajircewa a ayyukansu don kara ciyar da jami’ar gaba.

97 views0 comments
bottom of page