top of page
  • Writer's pictureArtv News

Jam'iyyar PDP a Kano ta gudanar da zaben fitar da gwani na gwamna guda biyu


A ranar Larabar da ta gabata ne jam’iyyar PDP a jihar Kano ta gudanar da zaben fidda gwani na takarar gwamna a kaso biyu, yayin da bangarorin biyu na jam’iyyar a jihar ke takun-saka na neman fidda gwani. Jaridar Tribune ta rawaito cewa,bangaren da ke karkashin Alhaji Wada Sagagi, bangaren masu biyayya ga tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso ne suka shirya taronsu a gidan Lugard, yayin da bangaren da ke karkashin Sanata Hayatu Gwarzo, bangaren dake biyayya ga Ambasada Aminu Wali suka gudanar da taron nasu a filin wasa na Sani Abacha. Sai dai ba a bayyana sakamakon bangarorin biyu ba har ya zuwa lokacin muka sanya wannan labari

256 views0 comments
bottom of page