top of page
  • Writer's pictureArtv News

Jahar Kano za ta amfana daga tsarin noman alkama na zamani na kasar Marocco

Daga Nura Sunusi Maliya

Jahar Kano karkashin Jagorancin Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje (OFR) ta tura mutane goma Sha biyu 12 zuwa kasar Morocco domin samun dabarun noman Alkama na zamani


A cewar mataimaki na musammam kan harkokin kafafen yada labari na ofishin mataimakin gwamna, Nura Sunusi Maliya, an samu nasarar gano dabarun noman Alkama daga manoman kasar Morocco ta yadda suke samun Alkama tan hudu a duk kadada daya, sabanin manomanmu da suke samun tan biyu a duk kadada daya. An kuma iya gano yadda manoma zasu yi noma ba tare da yi wa Kasar gona illaba (Zero tillage) ita wannan fasahar na baiwa manoni damar samun amfani mai yawa da kudi kalilan.



Tawagar Gwamnatin Kano dake Karkashin Jagorarcin mataimaki na musammam kan harkokin mulki na ofishin mataimakin gwamna, Dr. Mustapha Yusuf Abubakar da masu ruwa da tsaki a bangaran ci gaban noma a Jahar Kano.



Wannan dai na zuwa cikin Shirin nan na hadin Gwiwa tsakanin Gwamnatin Kano da Bankin duniya a cikin shirin nan na noma domin kyautatuwar rayuwa (Appeals Project Kano).


Tawagar da Shugabanin Shirin Appeals Project Kano suka dauki nauyin ziyarar ta hada da Shugaban Shirin Appeals Project na jihar Kano. Dr. Malam Hassan Ibrahim, Mustapha Bello, DG. Uba Danzainab, Ahmed Maradona Gawuna, Nura Sunusi Maliya, da Sauran Jami'an Shirin Appeals Project na Jihar kano.



Ana sa ran bayan wannan ziyara jahar Kano za ta amfana daga dimbun fasahar noman Alkama na zamani da kasar ta Marocco ta yi fice a kansa

38 views0 comments
bottom of page