top of page

Asarar da Saudiyya ke yi saboda rashin mahajjata daga kasashen duniya

Updated: Aug 4, 2021

Saudiyya na daga cikin manyan kasashen duniya da annobar cutar korona ta haifar da koma baya gahanyoyin samun kudaden shigarta




Saudiyya na samum ɗumbin kudaden shiga a lokutan ayyukan Hajji da Umara da miliyoyin Musulmai kan halarta a duk shekara daga kasashen duniya.

Kamar dai a shekarar bara, bana ma haka batun yake game da rage adadin wadanda za su halarci aikin hajjin, duk da cewa yawan ya ɗara na bara din.

Rashin zuwan mahajjata ƙasar daga ƙasashen duniya na nufin rage yawan kuɗaɗen shigar Saudiyya a fannoni da dama da suka haɗa da na sufuri da na otel-otel har ma fannin abinci da sauran kayayyaki.

A wannan maƙalar, BBC Hausa ta yi nazari kan irin asarar da rashin zuwan mahajjatan ƙasashen duniya ke jawo mata.

BBC ta tattauna da tsohon shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya, kuma masani kan harkokin da suka shafi ayyukan hajjin, Barista Abdullahi Mukhtar.

Masanin ya ce baya ga man fetur, babu wani abu da ke bai wa al'umma da kuma gwamnatin Saudiyya kuɗin shiga kamar ayyukan Hajji da Umara.

11 views0 comments

Recent Posts

See All
bottom of page