top of page
  • Writer's pictureArtv News

Ingila ta sha kashi mafi muni cikin shekaru 100


A karon farko cikin kusan shekaru 100, Ingila ta sha kashi mafi muni a gidanta a fafatawar da ta yi da Hungary wadda ta zazzaga mata kwallaye 4-0 a gasar Nations League ta Kasashen Turai.


Tun shekara ta 1928 rabaan da wata kasa ta yi wa Ingila irin wannan cin a gidanta, inda a wancan lokacin ta sha kashi a hannun Scotland da kwallaye 5-1. Tuni dai kocin tawagar Ingila Gareth Southgte ya fara shan matsin lamba, inda ake ganin cewa, ya kama hanyar kafa mummunan tarihi a matsayinsa na mai horas da kasar.

Yanzu haka yana da sauran wasannin da za su zame masa zakaran gwajin dafi gabanin soma gasar cin kfoin duniya a Qatar.

A bangare guda, Ita ma Jamus ta yi bijiji da Italiya da kwallaye 5-2 duk dai a gasar ta Ntions League.

Jamus ta zama kasa ta farko tun shekara ta 1957 da ta zura kwallaye 5 rigis a ragar Italiya a wasa guda.

Raban da Italiya ta sha irin wannan kashi, tun shekaru 65 da suka gabata, lokacin da Yugoslavia ta yi musu ci 6-1.

Mai tsaren ragar Italiya, Gianluigi Donnarumma ya ce, lallai sun yi bakin cikin wannan nasarar da Jamus ta samu a kansu, yana mai cewa, ba su da wani hanzari da za su kafa

28 views0 comments
bottom of page