top of page
  • Writer's pictureArtv News

INEC ta ba wa jam'iyyu wa'adin ba ta sunayen 'yan takarar shugaban kasa da mataimakinsu


Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, INEC, ta bai wa jam'iyyu wa'adin karshe na gabatar da sunayen mutanen da za su yi musu takarar shugaban kasa da mataimakansu.


INEC ta tsayar da 17 ga watan Yuni a matsayin ranar karshe na masu takarar shugaban kasa da mataimaka, da kuma sanatoci da 'yan majalisar tarayya.


BBC Hausa ta rawaito cewa, hukumar ta gargadi cewa da misalin 6 na yammacin Juma'a 17 ga watan Yunin, 2022 shafin da ake ciki sunayen 'yan takara zai rufe.


Sai dai na 'yan takarar gwamna da 'yan majalisar jihohi, a ranar 15 ga watan Yuli wa'adin zai cika.

65 views0 comments
bottom of page