top of page
  • Writer's pictureArtv News

Ifeanyi Okowa: Atiku ya zabi gwamnan Delta a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP


Dan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya zabi gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023.


Atiku ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis a wajen tantance ɗaukar ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasar a hedikwatar jam'iyyar da ke Abuja.


Dama an sanya ran cewa a ranar Alhamis ɗin ne jam'iyyun siyasar Najeriyar za su sanar da sunayen mutanen da za su mara baya ga 'yan takararsu na shugaban ƙasa.


A yayin da PDP ta fitar da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasar daga kudancin Najeriya, ita kuwa jam'iyyar APC mai mulki za ta ɗauko abokin tafiyar ɗan takararta ne daga yankin arewacin ƙasar.


BBC Hausa ta rawaito cewa Tuni dai jam'iyyar APGA ta fitar da abokin tafiyar ɗan takararta daga arewa ita ma.

An zaɓi mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasar na PDP ne ta hanyar kafa wani kwamiti don tantance mutanen da ke son mara wa ɗan takararta Atiku Abubakar baya.

7 views0 comments
bottom of page