top of page
  • Writer's pictureArtv News

Ibrahim Tanko Muhammad: Alkalin Alkalan Najeriya ya yi murabus


Rahotanni sun nuna cewa, Alkalin Alkalan kasar Mai Shari'a Ibrahim Tanko Muhammad ya yi murabus.


Wani makusancin Alkalin Alkalan ya tabbatar mana cewa babban Mai Shari'ar ya yi murabus ne jiya da daddare.


Murabus din nasa na da alaka da rikicin da ke faruwa tsakaninsa da manyan alkalan kasar 14 wadanda a makon jiya suka aike masa da wasika bisa zarginsa da rashin iya shugabanci, a cewarsa.


Kafofin watsa labaran kasar sun rawaito cewa alkalan sun zargi Mai Shari'a Tanko da kin daukar mataki duk da korafin da suka yi na rashin samun gidaje da motoci na aiki daga hukumomin kotun.


BBC Hausa ta rawaito cewa, makusancin Alkalin Alkalan, wanda ba ya so a ambaci sunansa, ya ce Mai Shari'a Ibrahim Tanko Muhammad, ba ya son ci gaba da ce-ce-ku-ce shi ya sa ya yar da kwallon mangwaro domin ya huta da kuda.


Ya kara da cewa tuni ya umarci mutumin da ya fi girman mukami a Kotun Kolin kasar ya karbi ragamar tafiyar da ita kafin a nada Alkalin Alkalai na dindindin.


Bayanai sun nuna cewa Mai Shari'a Olukayode Ariwoola shi ne alkali mafi girman mukami bayan murabus din Mai Shari'a Ibrahim Tanko Muhammad.


A watan Janairun 2019 ne shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya rantsar da Mai Shari'a Ibrahim Tanko Muhammad a matsayin mukaddashin Alkalin Alkalan kasar bayan dakatar da Alkalin Alkalan wancan lokaci, Walter Onnoghen bisa zargin da ya shafi kin bayyana kadarorin da ya mallaka.


Ya zuwa yanzu dai gwamnatin kasar ba ta fitar da sanarwar da ke tabbatar da yin murabus din Alkalin Alkalan Najeriya ba.

8 views0 comments
bottom of page