Artv News
Hukumar EFCC ta saki tsohon Gwamnan jahar Zamfara Abdul'aziz Yari

Wata majiya ta iyalansa, ta tabbatar da wannan ci gaba ga jaridar Daily Nigerian kamar yadda jaridar Daily News24 ta rawaito, inda ta ce an saki tsohon gwamnan ne a yammacin yau AlhamisF
An kama Yari ne a gidansa dake Unguwar Maitama a babban birnin tarayya Abuja dangane da zargin samun hannunsa cikin badakalar naira miliyan dubu tamanin da hudu da ake zargin tsohon Akanta Janar na kasa, Ahmed Idris.