top of page
  • Writer's pictureArtv News

Harin Kuje: An kama ’yan sanda suna waya da ’yan ta’addar da suka tsere


Dubun wasu ’yan sanda ta cika bayan an same su suna waya da ’yan ta’adda da suka tsere daga Gidan Yarin Kuje.


An kama ’yan sandan da ke kula da kes din (IPO) ’yan ta’addan ne bayan an tatsi sautin ganawarsu ta waya inda aka ji suna hada baki da ’yan ta’addar da suka tsere.


“Mutum biyu daga cikin ’yan ta’addan da suka tsere sun kira wani IPO suna wata tattaunawa da alamar hadin baki.

“Yanzu haka ana tsare da su ana bincikar su domin gano irin rawar da suka taka,” inji majiyarmu.


Dalilin Harin Kuje


Majiyar jaridar Aminiya ta ce ’yan ta’addar kungiyar ISWAP ne suka kai harin suka kubutar da mambobibsu daga gidan yarin, saboda Gwamnatin Tarayya ta ki amincewa da bukatunsu.


Ta bayyana cewa kungiyar da ta kai hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ce ta kai wa kurkun hari.


Ana zargin kungiyar Ansaru, wadda bangare ne na ISWAP, da kai harin jirgin kasan.


Majiyarmu ta ce kunguyar ta kai hari a gidan yarin ne bayan yunkurinta na amfani da fasinjojin jirgin wajen yin musaya domin gwamnati ta sako ’ya’yan mambobinta kuma mayakanta da ke tsare a Kuje da sauran wurare ya gagara.


“Da suka ga bukatarsu ba za ta biya ba, sai suka kai hari,” da ababen fashewa domin su samun saukin shiga gidan yarin.

Ta ce mayakan aka kubutar din za su fitini Najeriya idan ba a dauki matakin da ya dace ba.


An yi watsi da bayanan sirri


Bayanan da muka samu sun ce bayan jami’an hukumar gidajen yari da ke kula da cibiyar, sauran masu samar da tsaro a wurin sun hada da sojoji da ’yan sanda da SSS da Sibil Difens, saboda irin manyan masu laifi da ke tsare da gidan yarin.


Sai dai kuma hukumomi sun yi watsi da rahoton da aka samu kan yiwuwar harin, abin da ya ba wa maharan damar kutsawa cikin gidan yarin.


“Amma abin takaici shi ne ko’ina akwai baragurbi, saboda haka duk da cewa jami’an tsaro sun samu rahoto, ’yan ta’addar sun yi abin da suke so a cikin tsari, babu kuskure.


Yadda aka kai harin Kuje


“Wasu daga cikinsu sun rika tayar a ababen fashewa a wajen gidan yarin bayan sun rusa babbar kofar shiga, rukunin da aka tura ciki suka je suka kwaso mambobinsu ba tare da wata matsala ba.


“Wadanda suka shida gidan yarin kai-tsaye suka je sel din da ake tsare da ’yan Boko Haram suka sake su… Ba tare da wata turjiya ba,” a cewarta.


Majiyar ta bayyana cewa maharan sun yi amfani da nakiyoyi wajen balla gidan yarin, ciki har da bangaren da ake tsare da ’yan ta’adda, suka saki duk wadanda ke wurin.


“Hakika irin ’yan ta’addan da suka tsere za su addabi bangaren tsaron Najeriya da ma zaman lafiyar kasar idan ba a yi dauki matakin da ya dace ba.


“Kamar yadda ka gani ba su je bangaren da ake tsare da manyan mutane ba, domin ba su ne hadafin maharan ba.”


Wata majiya da ta zanta da wakilinmu ta ce, “Da gangan aka tsara harin domin sun san ba mu da karfin dakile hari a cikin dare.


“Saboda haka suka samu damar fito da mambobinsu suka kuma tafi da su.”


Yiwuwar sabbin hare-hare

Wata majita ta shaida mana cewa an gano ’yan ta’adda na shirin shirin kai hari ga Ofishin Runduna ta Musamman ta ’Yan Sanda (STS) wanda a baya ake kira Hedikwatar SARS da ke Abuja, inda suka kai wa hari a 2012.


Suna kuma shirin kai hare-hare a kan cibiyoyin soji da ke tsare da mambobinsu a Kainji da kuma gidajen yari da ke Bida da Minna a Jihar Neja.


“So suke su kubutar da mambobinsu da ke tsare a wadannan wuraren

“Suna so su aiwatar da wannan shiri ne a rabar Sallah, kuma muddin ba a dauki mataki ba, hakan za ta faru,” inji majiyar tamu.

453 views1 comment
bottom of page