top of page
  • Writer's pictureArtv News

Harin Jirgin Kasan Abuja-Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Ba Gwamnati Wa’adin Kwana 7


Yan bindigar da suka yi garkuwa da fasinjoji a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun ba wa gwamnati wa’adin kwana bakwai ta biya musu bukatunsu.


’Yan bindigar sun ba da wa’adin ne a sabon bidiyo da suka saki mai mai dauke da wasu mutum shida daga cikin fasinjojin da ke hannunsu.


’Yan bindigar sun zargi gwamnati da rashin gaskiya, kana suka ba ta wa’adin kwana biyar a kan su sako musu ’ya’yansu da suka ce ana tsare da su.


Da yake makagan, Mohammed Dehu, roko ya yi ga gwamnati ta saurari bukatun maharan don a kubutar da su.


Majiyarmu ta ce Sabon bidiyon ya nuna fasinjojin a cikin halin galabaita, ciki har da wani dan kasar Pakistan.

An ji daya daga cikin fasinjojin na cewa, “Sunana Mohammed, ma’aikaci a nan Najeriya amma dan asalin Pakistan, an yi garkuwa da mu ne a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga Maris, Mu 62 a nan.”


Kazalika, wani daga cikinsu ya ce, “Yanayinmu a nan sam babu dadi, don haka nake rokon Gwamnatin Najeriya da ta Pakistan da kungiyoyin kasa da kasa da su taimaka a kubutar da mu.”


’Yan uwan fasinjojin sun sha yin magiya ga Gwamnatin Tarayya a kan ta taimaka ta ceto musu ’yan uwansu cikin koshin lafiya.


Idan dai ba a manta ba, ko a makon da ya gabata an ji Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu, yana cewa, ana kan tattaunawa domin kubutar da fasinjojin da ke hannun ’yan bindigar.

5 views0 comments
bottom of page