top of page
  • Artv News

Hajjin bana: Gwamna Ganduje ya halarci taron gwajin aikin Haji ga maniyatan Kano

Daga Nura Ahmad Dakata

Gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci aikin Hajji na gwaji ga maniyata aikin Hajji na bana Wadanda suka fito daga jihar ta Kano.


Yayin da yake jawabi a wajen taron gwamna Ganduje ya bayyana cewa gwamnatin jihar kano ta gudanar da aiyuka masu yawa domin ganin maniyata aikin Hajjin bana sun sami kyakyawan yanayi da zasu gudanar da ibadar cikin sauki.


Ganduje yace kasancewa ibadar aikin Hajji na daya daga cikin shika-shikan addinin musulunci yasa gwamnatin da ta ke kashe magudan kudade wajen ganin an shirya yadda maniyatan kano zasu gudanar da aikin Hajjin cikin nutsuwa.Yace gwamnatin kano ta yi tanadin masaukai na alfarma kusa da harami a biranen makka da madakina , tare kuma da daukar nauyin malaman bita sama da dari 3 domin su koyawa maniyatan yadda ake ibadar tun daga nan kano har zuwa kasa mai tsarki.


Gwamna Ganduje ya kuma bada tabbacin gwamnatin kano bazata lamunci maniyaci daga kano ya zubar da kimar jihar da Nigeria a idon duniya ba.

“Mun kafa kotun tafi da gidan ka,wadda aka dora mata alhakin hukunta duk wanda yayi halin rashin da’a a kasa mai tsarki, duk da dai mun san mutanen kano suna da da’a sosai ,saboda sakamakon da’arsu tasa har muka sami lambobin yabo daga kasar saudiyya”. Ganduje


Ganduje ya kuma bukaci maniyatan dasu mai da hankali wajen yiwa kasa da kano addu’o’in samun zaman lafiya da ingantuwar tattalin arziki.A jawabinsa tun da fari sakataren zartar war hukumar jin dadin alhazai ta jihar kano Alhaji Muhd Abba Danbatta yabawa gwamna Ganduje yayi bisa yadda yake baiwa hukumar tallafi a duk lokacin da ta bukaci hakan, domin ingata aiyuka hukumar.


” Nasarorin da hukumar jin dadin alhazai ta jihar kano ta samu suna da nasaba da tallafi da damuwar da Gwamna Ganduje yayi da wannan hukumar ta mu”. Inji Danbatta


Wasu daga cikin malaman bita ne dai suka gudanar da aikin Hajjin na gwaji a bayyane bayan kammala bitar watanni 4, wanda hakan ke nuna an kammala bita baki daya ga maniyata aikin Hajjin bana a jihar kano.

8 views0 comments
bottom of page