top of page
  • Writer's pictureArtv News

Hajj2023: Hukumar Alhazai ta Kano Za Ta Kaddamar Da Fara Bita

Hukumar Jin dadin alhazai ta Jihar Kano na gayyatar Maniyyata aikin Hajjin wannan Shekara ta 2023 Maza da Mata halartar Bikin Bude Bitar Mako-Mako.

Za a rinka gudanar da Bitar ne a ranakun Asabar da Lahadi Wanda a Cibiyar Bita ta S A S da Kuma sauran Cibiyoyin Bita 15 da ke fadin Jihar Kano


A sanarwar da mataimakiyar Daraktan Wayar da kai da ilmantar da Alhazai ta Hukumar, Hajiya Hadiza Abba Sunusi ta fitar, ta ce za a bude bitar a ranar Asabar 4 GA watan Fabarairu na shekara ta 2023 da karfe goma na safe


Sanarwar ta yi kira ga dukkanin maniyyata aikin Hajin na bana da su tabbata sun halarta

64 views0 comments
bottom of page