Artv News
HAJJ2022: Hukumar alhazai ta Kano ta yi tanadi na musammam don duba lafiyar maniyyata

Daga cikin shirye-shiryen da hukumar ke kokarin karasawa a yanzu, sun hada da aikin gyaran rumfunan da iska ta lalata a sansanin alhazai da sanya kayan aiki a sabon asibitin alhazai dake sansasanin da dai sauransu.

Za iya tunawa cewa an samar da sabon asibitin ne ta karkashin Shirin da ake ajiye wasu daga cikin kudaden alhazai (Development levy) da nufin saukakawa maniyyata dukkanin wasu wahalhalun da sukan fuskanta a dukkanin lokacin da bukatar harkar kula da lafiya ta taso.
Wannan ci gaba ya samu ne sakamakon irin jajircewar da bibiyar dukkanin masu ruwa da tsaki da sakataren zartarwa na hukumar kula da jin dadin alhazai ta Jahar kano, Alhaji Muhammad Abba, yayi tare da samun cikakken goyon bayan gwamnan Jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.

A yanzu haka dai tuni Alhaji Muhammad bba Danbatta ya nemi sahalewar gwamna Ganduje domin samar da dukkanin kayan aiki da magunguna da na’urori domin fara amfani da asibitin don yin dukkanin wasu gwaje-gwaje da ake yi wa maniyyata aikin haji a duk lokaci irin wannan

An kuma samar da dukkanin ma’aikatan da zasu gudanar da aikin wanda kuma bayan kamala aikin haji za a rinka amfani da shi domin bukatar sauran al’uma baki daya.
A wani labarin kuma, za a iya tunawa cewa a kwanakin baya ne, gwamna Abdulahi Umar Ganduje ya amince a gina sabon masallacin juma’a a sansanin alhazai na kano tar da samar da bandakuna wadatattu da kuma gyara babbar rumfar da iska ta lalata a filin gwajin aikin haji dake sansanin na alhazai.

Bisa wannan dalili ne, Sakataren zartarwa na hukumar alhazan, ya ziyarci sansanin domin duba yadda filin da za gina masallacin da bandakunan da kuma rumfar da ta lalace
Bisa yunkurin, wakilinmu Nura Ahmad Dakata ya ziyarci sansanin alhazan inda ya tarar tuni aikin gina masallacin da na bandakunan sun yi nisa kuma shi ma aikin gyaran rumfar ana kan gudanar da shi a halin yanzu.

A binciken da wakilin namu ya yi, ya nuna mana cewa, Alhaji Muhammad Abba Danbatta ya bayar da umarnin gaggauta kammala aikin, musamman na rumfunan wanda a yankun ya kai kaso casa’in cikin dari domin gab ake da gudanar da gwajin aikin haji a aikace wanda daga shi ne kuma mainiyyatan Jahar kano zasu fara tashi zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da aikin hajin bana