Artv News
#HAJJ2022: Hukumar alhazai ta Kano ta kafa kwamitin tsaro don sanya idanu kan aikin Hajin bana
Daga Nura Ahmad Dakata

Da yake gabatar da jawabi a yayin ziyarar babbar cibiyar bitar alhazai dake makarantar koyar da harshen larabci ta SAS, shugaban kwamitin tsaron, wanda kuma ya kasance mukaddashin Konturola na hukuamr lura da shige da fice ta kasa, Mustapha Fagge, yace hukumar kula da jin dadin alhazan karakashin shugabancin Alhaji Muhammad Abba Danbatta, ita ce ta kafa kwamitin wanda ya kunshi jami’an hukumar lura da shige da fice ta kasa da jami’an ‘yan sanda

Sauran sun hada da da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya da na hukumar wayar da kawunan al’uma ta kasa da na hukumar yaki da sha da fataucin muyagun kwayoyi ta kasa da hukumar yaki da safarar mutane da na kotun tafi da gidanka ta alhazai da na kungiyar dake taimakawa alhazai
Mustapha Fagge ya ja hankalin maniyyatan da su tabbata sun yi kaffa kaffa da fasfo dinsu don gujewa bacin ran da zai biyo sakamakon batansa a hannunsu
Ya kara da cewa dukkanin wadanda jam’ai karkashin jagorancinsa, zasu yi aiki tukuru domin tabbatar da ganin cewa Jahar kano ta ci gaba da rike kambunta a fannin tabbatar da tsaro a lokacin aikin haji tun daga nan gida Najeriya har zuwa kasa mai tsarki

Shi ma da yake nasa jawabin a madadin Kotun tafi da gidanka ta alhazai, mai sharia’ Alhaji Salisu Muhmmad Isah, yace an kafa Kotun ce domin hukunta dukkanin wani alhaji da ya karya doka a lokacin aikin haji
Sai dai mai sharia’ yayi fatan har a kamala aikin hajin na bana ba za a samu ko da mutum daya da zai yi laifin da kotun za ta hukunta shi ba
Tunda farko a nasa jawabin, daraktan kula da ayyukan haji na hukumar alhazai ta kano, Alhaji Kabiru Panda, yace a kowacce shekara hukumar ta kan kafa wannan kwamiti domin tabbatar da bin doka da oda a tsakanin alhazan tun daga gida Najeirya har zuwa kasa mai tsarki.
Kwamitin ya ziyaraci cibyar bita ta mata dake makarantar koyar da haddar Alkur’ani mai tsarki da yankin karamar hukumar tarauni