Artv News
Hajj2022: Hukumar alhazai ta Kano na taba alli da NAHCON kan kamfanin da zai yi jigilar alhazanta
Daga Nura Ahmad Dakata

Sakataren zartarwa na hukumar, Alhaji Muhammad Abba Danbatta ne bayyana haka, yayin da yake yi wa manema labarai jawabi dangane da shirye-shiryen hukumar kan fara jigilar maniyyata aikin hajin bana
Za a iya tunawa cewa an samu cece-kuce bayan NAHCON ta hada Kano a cikin jihohin da kamfanin Azman Air zai yi jigilar maniyyata a lokacin aikin Hajjin 2022.
Rahotanni daga kafafen yada labarai sun ce hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta ki amincewa da kamfanin Azman Air a matsayin jirgin da ya yi jigilar maniyyata.
Sai dai sakataren zartarwa na hukumar Alhaji Muhammad Abba Dambatta, wanda ya yi wa manema labarai jawabi, ya ce batun kin amincewa da shi bai taso ba, domin tun farko jihar ba ta taba neman aikin kamfanin na Azman Air ba.
Ya ce hukumar ba ta taba rubutawa ko kulla huldar aiki da Azman Air ba, ya kara da cewa ba su taba neman kamfanin ya dauke maniyyatansu ba
Dambatta ya ce hukumar na ci gaba da tattaunawa da NAHCON kan kamfanin jirgin sama domin jigilar maniyyatan Kano.
Sakataren zartarwar ya kara da cewa nan da sa’o’i 24 masu zuwa za a fitar da sanarwar kan jirgin da za a yi amfani da shi wajen jigilar maniyyatan jihar kano.