top of page
  • Writer's pictureArtv News

#hajj2022: Maniyyata na hawan Arfah a Saudiyya


Yau ne alhazai ke fita filin Arfa a ci gaba da gudanar da ayyukan hajjin bana.


Kimanin alhazai miliyan guda ne suka fita domin tsayuwar ta arfa inda za su kwashe yinin ranar wato tun daga zawali zuwa faduwar rana suna addu’oi kafin daga bisani su wuce zuwa Musdalifa.


Ranar Arfa ita ce rana mafi girma da muhimmnanci a duka kwanakin aikin hajji. Ko a hadisi ma ya zo, Annabi SAW yace Arfa ita ce hajji.


Don haka duk alhajin da bai shiga filin arfa ba har rana ta fadi a yau to ba shi da aikin hajji, sai ya sake.

Hakan ta sa a kowane irin hali mutum ya ke ciki sai ya je filin, hatta ma marasa lafiya ana kai su.


Hukumomin Saudiya sun yi wani tanadi na daukar marassa lafiya da ke cikin mawuyacin hali a kai su filin a cikin motocin daukar marassa lafiya, domin su dace da samun ranar.


A Arfah dai alhazai suna hada sallar Azahar da La’asar, kuma raka’a bibbiyu.


Daga nan za su zauna suna ta addu’o’I da karatun kur’ani da zikiri har zuwa faduwar rana.

Idan rana ta fadi kuma ba za su yi sallar magriba a filin Arfa ba, sai su kama hanyar tafiya Muzdalifa.


Muzdalifa shi ma wani fili ne mai girman gaske da ke tsakanin filin Arfa da Muna a kan hanyar zuwa Makka.


Kuma da zarar an fita daga Arfa, Muzdalifa za a shiga, kamar yadda ana fita daga Muzdalifa to an shiga Muna ke nan, inda nan ne alhazai kan yi kwanaki yayin aikin hajji.


A wannan shekarar 2022, arfa ta fado a cikin ranar Jumma’a, kuma ba kasafai ake samun ranar ta fado a Jumma’ar ba.


Haka kuma za a yi hawan arfa na 2022, ne bayan shafe shekara biyu alhazai daga wasu kasashe ba su halarci aikin hajji ba saboda bullar annobar korona.


Hakan ne y asa hukumomin Saudiyya suka kayyade adadin mahajjatan shekarar zuwa miliyan guda.

11 views0 comments
bottom of page