top of page
  • Writer's pictureArtv News

Gwamnatin Katsina ta shirya addu’a ta musamman kan matsalar tsaro


Gwamnatin jihar Katsina ta shirya wani taro na musamman na addu’o’i domin roƙon rahamar Allah da kuma neman Ya yaye rashin tsaro da ke addabar jihar da ma ƙasa baki ɗaya.


Sheik Abidu Yazid, shugaban babban kwamitin taron ne ya bayyana haka a wajen taron addu’o’in na 2022 da aka yi a Katsina a yau Litinin.


Malam Yazid ya ce an shirya taron ne domin godiya ga Allah bisa ni’imominsa da kuma neman ɗauki gare Shi a bisa halin rashin tsaro da ke addabar jihar da ma kasa baki daya.


Ya ce Allah ya jarrabi annabawa da al’ummomin da suka gabace mu da bala’o’i daban-daban a lokuta daban-daban amma kuma sun samu galaba a kansu, inda ya kuma a ka yi addu’ar Allah Ya sa Nijeriya ta ci galaba a kan nata matsalolin.


Tun da fari, a nasa jawabin, Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari, ya godewa malaman addinin musulunci da suka halarci taron addu’ar na musamman.


Masari ya bukaci jama’a da su rika yin addu’a a duk halin da suka samu kansu.

(DNH)

6 views0 comments
bottom of page