top of page
  • Writer's pictureArtv News

Gwamnatin Kano ta hana zirga-zirgar Adaidaita sahu bayan karfe 10 na dare


Gwamnatin jihar Kano ta sanar da hana zirga-zirgar babura uku wanda da aka fi sani da A Daidata Sahu bayan karfe 10:00 na dare daga ranar Alhamis 20 ga watan Yuli, 2022.


Sanarwar da kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba ya fitar ta nuna cewa an cimma matsaya kan hakan ne a karshen taron Majalisar tsaro ta jihar Kano.


Ya ce matakin wani bangare ne na kokarin tabbatar kare rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar.


Kwamishinan, a cikin sanarwar, ya bukaci masu tuka baburan masu uku da su bi umarnin, kuma su daina aiki a lokacin da aka kayyade domin jami’an tsaro za su aiwatar da dokar ba tare da wata matsala ba.


116 views0 comments
bottom of page