top of page
  • Writer's pictureArtv News

Gwamnatin jihar Kano ta rufe makarantun kiwon lafiya 26 marasa lasisi


Gwamnatin jihar Kano ta rufe wasu makarantun koyar da harkokin kiwon lafiya 26 da ba su da lasisi a jihar.


A wata sanarwa da hukumar lafiya ta jihar ta aike wa manema labarai, mai ɗauke da sa hannun jami'ar hulda da jama'a ta ma'aikatar Hajiya Hadiza Namadi ranar Juma'a.


Ta ce makarantun za su ci gaba da kasancewa a rufe sai bayan kammala gudanar da bincike a kansu.


Sanarwar ta ƙara da cewa wasu daga cikin makarantun ba su da mazauni na dindindin, sannan kuma suna koyar da wasu kwasa-kwasai da suka saɓa da tsarin manhajar koyar da kiwon lafiya, tare kuma da tatsar dalibai da iyayensu maƙudan kuɗaɗe na babu gaira-babu-dalili.


A ƙarshe sanarwa ta shawarci mazauna jihar da su guje wa irin waɗannan makarantu, ta hanyar zuwa makantun da gwamnati ta bai wa lasisi.

108 views0 comments
bottom of page