top of page
  • Writer's pictureArtv News

Gwamnati ta gaza wajen kare 'yan Najeriya - Masari


Gwamnan jihar Katsina a Najeriya, Aminu Bello Masari ya ce gwamnati da hukumomin tsaron kasar sun gaza wajen kare rayukar ‘yan Najeriya. Masari, na daga cikin gwamnonin da ayyukan ‘yan bindiga masu satar shanu da mutane da kuma kisa suka wa katutu.

Jaridar ‘Daily Trust’ ta ruwaito cewa, a yayin da ya ke mayar da martani a kan matsalar tsaro da ta addabi sassan kasar, Masari ya ce jami’an tsaro da gwamnati sun gaza kare mutanen da suka dogara da su don samun kariya. Sai dai Masari ya ce an fara samun sauki ida aka kwatanta da yadda al’amarin yake kafin yanzu, amma ya kara da cewa ba a kai inda ake harin kaiwa ba.


Ya kuma bayyana cewa Najeriya za ta yi nasara wajen shawo kan matsalar tsaro da ke ci mata tuwao a kwarya kafin ta mika mulki ga gwamnati mai zuwa.


11 views0 comments
bottom of page