top of page
  • Writer's pictureArtv News

Gwamnati Ta Dauki Malaman Darasin Tarihi 3,700


Gwamnatin Tarayya ta dawo da darasin tarihi a makarantun firamare da sakandare bayan shekara 13 da sokewa.


A halin yanzu gwamnatin ta dauki malaman bangaren guda 3,700 domin ba su horo da nufin inganta koyar da darasin a shekarar 2009/20210.


Babban Sakataren Hukumar Kula da Ilimi a Matakin Farko (UBEC), Hamid ya ce an dauki malaman ne a jihohi 36 da Birnin Tarayya, inda a kowace jiha aka dauki mutum 100.


Da yake jawabi a taron kaddamar dawo da darasin da kuma horas da malaman, Ministan Ilimi Adamu Adamu ya ce dakatar da darasin da aka yi a baya ya haifar da karuwar lalacewar tarbiyya da raya al’adu.


Adamu Adamu, ya bayyana haka ne ta bakin Minista a Ma’aikatar Ilimi, Goodluck Opiah, a taron, wanda ya wakilce shi a taron da Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar da sauran masu ruwa da tsaki suka halarta.


A jawabinsa, Sarkin Musulmi, ya yi kira ga sarakunan gargajiya da sauran ’yan Najeriya da su taimaka tare da goyon bayan gwamnatin kan dawo da darasin tarihi a makarantun firamare da sakandare.

22 views0 comments
bottom of page