Artv News
Gwamna Ganduje zai rantsar da sababbin kwamishinoni a ranar Juma'a

Gwamnan jihar Kano, Dr.Abdullahi Umar Ganduje zai rantsar da sababbin kwamishinoni tara a ranar Juma’a 2 ga watan Satumba. Wadanda majalisar dokokin jihar ta tantance tare da amincewa da nada su, za su maye gurbin mambobin majalisar zartaswar jihar da suka yi murabus domin neman mukamai a zaben 2023 mai zuwa. Sanarwar da kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba ya fitar ta nuna cewa an shirya gudanar da bikin rantsarwar ne a filin wasa na Sani Abacha Indoor da ke kofar Mata Kano da karfe 2:00 na rana. Gwamnan zai bayyana ma’aikatun su daga baya bayan rantsar dasu Wadanda za a rantsar sun hada da Malam Ibrahim Dan’Azumi Gwarzo, Alhaji Abdulhalim Abdullahi, Hon. Lamin Sani Zawiyya, Hon. Ya'u Abdullah , Hon Yusuf Abubakar. Sauran su ne Dr. Yusuf Jibrin Rurum Ali Musa Hamza da Adam Abdu Fanda Aminu Ibrahim Tsanyawa da Hon. Saleh Kausani da Alhaji Kabiru Mohammed