top of page
  • Writer's pictureArtv News

Ganduje ya samu lambar yabo ta zama wanda ya fi kowanne Gwamna bayar kulawa kan aikin hajin 2020

Daga Nura Ahmad Dakata

Taron wanda kungiyar 'yan jaridu masu daukar rahotannin aikin haji ta kasa tas shirya, an gudanar da shi ne a dakin taro na babban masallacin kasa dake Abuja


Laccar aikin Hajji na 2022 da lambar yabo mai taken Jarumai na Hajjin 2022, an yi shi ne don bayyana wadanda suka tsallake kalubalen da ba a taba gani ba na aikin hajjin 2022 tare da bayar da kyakkyawar hidima ga Mahajjatansu.


Da yake gabatar da jawabi, daya daga cikin wadanda aka karrama, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje wanda mataimakinsa Dr Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta, ya yaba da kokarin hukumar alhazai ta Najeriya bisa shirye-shiryen da aka yi a yayin gudanar da aikin Hajjin da aka kammala duk da cewa an samu kalubaleDr Abdullahi Umar Ganduje ya yi amfani da taron wajen yin kira ga masu ruwa da tsaki a kan su kara himma wajen wayar da kan maniyyata, inda ya jaddada cewa, jihar Kano ta fara shirye-shiryen gudanar da aikin hajjin na gaba.


Gwamna Ganduje ya bayyana wa mahalarta taron cewa Kano ta fi tsarin wayar da kan Alhazai a duk fadin kasar nan wanda ake gudanar da shi kafin a yi aikin Hajji da lokacin gudanar da shi da kuma bayan kammala shi.


Gwamnan ya yi nuni da cewa, babu shakka wannan karramawar za ta sa shi da duk wadanda aka karrama su kara kaimi wajen inganta jin dadin Alhazansu domin gudanar da aikin Hajjin su cikin kwanciyar hankali.


A nasa bangaren, Sakataren Zartarwa na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Muhammad Abba Danbatta, wanda shi ma ya karbi lambar yabo na Shugaban Hukumar Alhazai da ya fi kowanne iya tafiyar da harkokin gudanarwa a duk Najeriya, ya yi godiya ga kungiyar ‘yan jarida masu zaman kansu dake daunar rahoton aikin Hajji da suka ga cancanci a ba shi wannan lambar yabo.Dambatta ya yi amfani da taron wajen jinjina wa Gwamna Ganduje bisa goyon bayan da yake bai wa hukumar wanda ya bayyana a matsayin kashin bayan nasarorin da Kano ta samu kawo yanzu ta fuskar ayyukan Hajji.


Tun da farko, Babban jami’in kungiyar yan jaridun masu daukar rahoton aikin haji ta kasa, Alhaji Ibrahim Muhammad, ya ce sharuddan kungiyar na wannan shekara da aka karrama ba wai kawai sun ginu ne a kan gudanar da aikin Hajjin 2022 kadai ba, sai dai ya hada da jadawalin yadda hukumomin Alhazai na Jihohi ke tafiyar da ayyukan Hajji. a lokacin gwajin cutar covid 19


Daga nan sai ya yi kira ga sauran gwamnonin jihohi da su ba su goyon baya tare da kwadaitar da hukumomin Alhazai na su domin gudanar da aikinsu na farko yadda ya kamata.


22 views0 comments
bottom of page