top of page
  • Writer's pictureArtv News

Ganduje ya nada Baffa Dan Agundi a matsayin shugaban riko na hukumar kare hakki masu siyan kaya


Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya amince da nadin Manajan Darakta na Hukumar KAROTA, Baffa Babba Dan Agundi a matsayin mukaddashin Manajan Darakta na Hukumar Kare hakkin masu siyan Kayayyakin (KSCPC), har zuwa lokacin da za a nada Manajan Darakta. . Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa tsohon Manajan Darakta na hukumar, Janar Idris Bello Dambazau (Rtd) ya yi murabus daga mukamin nasa a kwanan baya bayan da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar ta fara bincikarsa An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar, ya fitar a ranar Litinin. Sanarwar ta ce nadin ya fara aiki ne nan take. “A matsayinsa na mukaddashin shugaban hukuamar, Baffa zai duba dukkan sassan hukumar, na aiki da sauran su, da nufin ganin an samar da yanayi mai kyau, kafin a nada Manajan Darakta,” in ji sanarwar.

239 views0 comments
bottom of page