top of page
  • Writer's pictureArtv News

Ganduje ya fiye mana duk wani hadimin Buhari marar amfani-Mudassir Kassim



Ku wadannan matasa dake kiranku hadiman Buhari yau dai an koya muku wani karatu da baku sani ba cikin darasin siyasa.


'Yan kudaden da kuka tara kuka hana halattattun masoya Buhari kuka ki taimakonsu, yau kam ga shi anci kudin a banza an kuma yada kwauren ganganku.


Kuna kallo ana zagin Buhari akan abinda kun fi mu sanin hakikanin yadda yake, amma sai in kun ga mun fara karewa sannan ku fito kuna chaaa! Wani lokacin ma maganarku don kare Buhari dagula lamurra suke yi don ba kwa maganar yadda ta dace.



Ashe wai don kuna da (ambition) na takara ne wai don kar kuyi bakin jini a zageku. Mu kun bar mu da shan zagi a wajen mutane ba kuma albashi balle tumunin siyasa.

Mu Ganduje ya taimakemu fiye da duk wani dake kiran kan shi hadimin Buhari.

Don haka yanzu sai ku girbi abinda ku ka shuka. Ku zo ku fara siyasa daga gras root ba taka haye ba.

Bashir Ahmad Shaaban Sharada #GarbaShehu #shaabansharada #barristerismaeel

55 views0 comments
bottom of page