top of page
  • Writer's pictureArtv News

Ganduje Ya Fita Hakkin Al'ummar sa ta Jihar KanoDaga Aminu DahiruA Ranar Alhamis 27 ga watan Mayu ne mataimakin gwamnan Jihar kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya lashe zaben fidda d’an takara gwamna na jam’iyyarmu ta APC mai albarka.


Yanzu ta tabbata Dakta Nasiru Yusuf Gawuna shi ne ‘dan takarar gwamna a inuwar jam’iyyar APC a wannan jiha a zaben shekara mai zuwa ta 2023, a yayinda tsohon komishinan kananan hukumomi na jihar, Alhaji Murtala Sule Garo zai mara masa baya.


A zahiri Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya fita hakkin al'ummar sa ta Jihar Kano. Bayan ayyukan more rayuwa da ya shekara bakwai da wasu watanni yana bijurowa da wannan jiha mai dimbin tarihi tun lokacin da aka zabe shi karo na farko a matsayin gwamnan jihar a shekarar 2015, gwamnan bai yi kasa a gwiwa ba. Babban burinsa shi ne ya tabbar ya zabar wa al’ummar Jihar kano wadanda za su gajeshi su kuma dora bisa ayyukan raya kasa da cigaban jihar kano wanda gwamnatinsa take aiwatar wa tsawan wannan lokaci.


Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya dade yana burin samar wa da wannan jiha mai albarka taswira ta tsarin mulki a matsayin alkibilar ga duk wanda zai mulki jihar bayan ya sauka daga kan karagar mulki.


Irin wannan taswira ita ce Iko (Jihar Legas) ke tutiya da ita a yau; haka zalika wannan tsari ya taimaka wa jihar wajen kaiwa gaci a fannoni da dama.


Rashin samun tsayayyun mutannan da za su dora akan wannan kadami na iya jefa Jihar Kano cikin wani mawuyacin hali, ya kuma dawo da jihar baya.


Irin wannan dalili ne ya sa gwamnan ya zakulo wadan nan matasa guda biyu wadan da zukatansu ke cike da kishin Jihar Kano, kuma a shirye su ke da su bautawa jihar dan cigabanta musamman bunkasa rayuwar matasa da mata wadan da su ne kashin bayan kowace al’umma.


Ko kafin wannan lokaci an jarraba Dakta Nasiru Yusuf Gawuna da Alhaji Murtala Sule Garo a matakai daban daban na mulki an kuma tabbatar da ingancinsu da zurfin tunaninsu.


Dan haka lokaci yayi da al’ummar Jihar Kano za su mara wa wadannan matasa baya dan cigaban wannan jiha tamu mai albarka.

43 views0 comments
bottom of page