top of page
  • Writer's pictureArtv News

'Fursunoni 300 sun tsere daga gidan-yarin Kuje'


Tsaron Najeriya, Bashir Magashi, ya ce kimanin fursunoni 600 ne suka tsere a yayin harin da aka kai gidan-yarin Kuje da ke Abuja ranar Talata da daddare.


Ministan, wanda ya tabbatar wa BBC wannan labarin, ya kara da cewa kusan 300 daga cikinsu sun mika kansu ga hukumomi don radin kansu yayin da jami'an tsaro suka kamo wasu daga cikinsu.


Ministan ya dora alhakin harin kan kungiyar Boko Haram, yana mai cewa akwai kimanin mayakan kungiyar akalla 64 a gidan-yarin lokacin da aka kai harin.


Magashi ya kuma tabbatar da mutuwar jami'in Civil Defence daya.


Sai dai sanarwar da hukumar da ke lura da gidajen-yari ta Najeriya ta fitar ta ce fursunoni 879 ne suka tsere yayin da aka kai harin.


Sanarwar, wacce mai magana da yawun gidan-yarin, Abubakar Umar ya sanya wa hannu, ta ce wasu fursunoni sun koma don radin kansu amma kawo yanzu ana neman fursunoni 443.


A cewarsa, fursunoni hudu sun mutu yayin da 16 suka jikkata.


Hukumomi sun ce a halin yanzu komai ya lafa a gidan-yarin kuma jami'an tsaro sun sake karbe iko da kurkukun.


Harin na zuwa ne 'yan sa'o'i bayan da 'yan bindiga a Katsina suka yi wa kwambar motocin Shugaba Muhammadu Buhari kwanton-bauna a kan hanyarsu ta zuwa garin Daura, mahaifar shugaban kasar.

2 views0 comments
bottom of page