top of page
  • Writer's pictureArtv News

Firaministan Birtaniya ya tsallake rijiya da baya


Firaministan Burtaniya Boris Johnson ya tsallake rijiya da baya a kuri’ar yankan kauna da ‘yan majalisar kasar suka kada domin tsige shi ko kuma tabbatar da ci gaba da kasancewarsa a karagar mulki. Wannan dai na zuwa ne, bayan da ya samu kuri’u 211 daga ‘yan majalisar da ke neman kasancewarsa a kan mukamin yayin da 148 suka nemi a tsige shi.

Sakamakon na nufin Johnson ya tsallake rijiya da baya a kuri'ar amincewa ko kuma rashin amincewa da jam'iyyarsa ta masu ra’ayin rikau ta kawo.

Amma takaddamar shagalin game da abubuwan da suka faru lokacin dokar kulle a Downing Street, hakan ya sanya ya zama Fira Ministan Burtaniya na farko da ya karya doka, da ake ganin hakan ya haifar da nakasu ga martabarsa.

A kuri'un da masu ra’ayin rikau suka kadawa, magabata irin Margaret Thatcher da Theresa May duk da cewa sun sha da kyar, amma daga karshe sun yi murabus.

Bayan ya tsallake rijiya da baya a zaben na ranar Litinin, Boris Johnson zai iya ci gaba da zama shugaban jam'iyyar Conservative da kuma matsayinsa na Fira minista.

A karkashin dokokin yanzu, ba za a bar 'yan majalisar masu ra’ayin rikau su sake gudanar da kuri'ar yankar-kauna ba har tsawon shekara guda.

24 views0 comments
bottom of page