Artv News
Fayemi zai iya rike kowanne irin mukami-Ganduje

Gwamnan jihar Kano Dr.Abdullahi Umar Ganduje ya ce halayya ta asali, hangen nesa da basirar da gwamnan jihar Ekiti Dr.Kayode Fayemi ke dasu, zasu sashi iya rike duk wani mukamia Najeriya
"Abubuwan da suka gabata suna da kyau domin kana cikin wadanda ke sa mutum yin alfahari da kasancewa a jam'iyyar APC" inji shi"
Ya bayyana hakan ne a ranar AlhamiS a wata ziyarar tuntuba da ya kai masa Kano da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC kuma shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya domin tattaunawa da wakilai a fadar gwamnati.

Gwamnan wanda mataimakinsa Dr.Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta, gwamnan ya kara da cewa jam'iyyar APC a Kano ba za ta manta da gudummawa, hadin kai da kuma goyon bayan da Dr.Fayemi ya bayar domin ganin ya samu nasara a zaben 2019 ba
"Kai ne Gwamna daya zo ya ganmu a yayin sake zaben, muna godiya kwarai da gaske ya ce ".
Gwamnan ya ci gaba da cewa muna fata fatan alheri da nasara a lokacin zabukan fidda gwani na shugaban kasa na jam'iyyarmu.
Tun da farko gwamnan jihar Ekiti Dr.Kayode Fayemi yace yaje kano ne domin neman goyon baya da kuma tattaunawa da shuwagabannin jam'iyyar da masu zabe.
"Kano APC ce, APC kuma Kano ce"
"Ni dan jam'iyyar APC ne wanda ya yi aiki a mukamai daban-daban don haka na zo muku da gogewar da ake bukata"
"Na zo muku ne domin in yi muku bayani kan manufar da nake da ita ta sabuwar Najeriya domin ku dora ni. akan sikelin mutanen da kuka gane suna da manufa ta cigaba don haka ina kira gareku da ku hada hannu da ni wajen tunkarar kalubalen da ake fama da shi a kasar nan Fayemi yace"