top of page
  • Writer's pictureArtv News

Europa League: Man United za ta kara da Sociedad, Arsenal da PSV


Hukumar kwallon kafa ta Turai UEFA ta gabatar da taron raba rukuni na kungiyoyin da za su buga gasar Europa ta 2023.


Cikin wani kayataccen biki da ya gudana a Istanbul na Turkiyya, an rarraba kungiyoyin zuwa rukunai takwas, wadanda suke dauke da kungiyoyi 32 baki daya.


Manchester United da ke rukunin E za ta fafata da Real Sociedad ta Sifaniya da FC Sheriff daga Maldova sai kuma Omonia daga Cyprus.


Manchester United da ta lashe gasar a 2017, ta buga wasa da Real Sociedad a matakin rukuni a Champions Lig a 2013.


AS Roma da ta lashe kofin Confederation a karon farko a bara, ta na jan ragamar rukunin C za ta buga wasa da Ludogorets da Real Betis sai kuma HJK Helsinki daga kasar Finland.


Arsenal da ke rukunin A za ta fafata da PSV da Bodø/Glimt sai kuma Zürich, rukunin da ake ganin shina za a yi fafatawa mai zafi a cikinsa.

9 views0 comments
bottom of page