top of page
  • Writer's pictureArtv News

EU zata kammala nazarin shigar da Ukraine cikinta a makon gobe


Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce a makon gobe majalisar zartaswarta zata kammala shawarwari kan amincewa ga Ukraine takarar neman shiga kungiyar Tarayyar Turai. Von der Leyen ta bayyanawa shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky haka yayin wata ziyarar ba-zata da ta kai birnin Kyive, , yayin da shugaban kasar Volodymyr Zelensky ya gargadi duniya da kada su yi watsi da rikicin da ke neman kawo karshen kasarsa.

Ursula von der Leyen ta ziyarci kasar Ukraine ne a wannan Asabar, domin tattaunawa kan fatan kasar na shiga kungiyar EU.

Ziyarar Von der Leyen itace ta biyu tun bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu – wanda ke zuwa yayin da ake ci gaba da gwabza kazamin fada a gabashi da kudancin Ukraine.



4 views0 comments
bottom of page