top of page
  • Writer's pictureArtv News

Elon Musk Ya Yi Barazanar Fasa Sayen Twitter



A wata wasika da lauyoyinsa suka fitar a ranar Litinin, attajirin ya ce matukar ba a ba shi wasu cikakkun bayanai kan shafukan bogi da ke dandalin ba, akwai yiwuwar cinkin ya sami matsala.


Jaridar Aminiya ta rawait cewa, hakan dai a cewarsa ya saba da yarjejeniyar da suka kulla da su tun a farko.


“Wannan karara ya saba da matsayar da muka cim ma da su ta samar da bayanai ba tare da kumbiya-kumbiya ba,” inji shi.


Sai dai kamfanin na Twitter a cikin wata sanarwa ranar Litinin ya ce yana fatan ganin cinikin ya kammala a kan farashin da aka amince tun da farko.


A watan Afrilun 2022 ne Hukumar Gudanarwar Twitter ta amince da murya daya ta sayar wa Elon Musk dandalin, ko da yake yarjejeniyar ta bukaci amincewar masu hannun jari a kamfanin.


A wata sanarwa yayin sayen kamfanin dai, Elon Musk ya ce dakatar da amfani da shafukan bogi ne zai kasance cikin manyan abubuwan da zai fi mayar da hankali a kan su da zarar cinikin ya fada.


Sai dai a watan da ya gabata, attajirin ya sanar da jinkirta kammala cinikin har sai an daddale batun.

8 views0 comments
bottom of page