top of page
  • Writer's pictureArtv News

Dangin fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna na zanga-zanga a Ma'aikatar Sufuri



Iyalai da dangin fasinjojin jirgin kasar nan da aka sace 'yan uwansu yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Kaduna da ke Najerya sun sa ke gudanar da zanga-zangar inda suke kira ga gwamnati ta ceto 'yan uwansu.


Hakan na faruwa ne kwana guda bayan bullar wani bidiyo da ke nuna yadda 'yan bindigar suke lakada musu duka.


Yayin zanga-zangar da suka gudanar da safiyar Litinin din nan a Ma'aikatar Sufuri ta Najeriya da ke Abuja, dauke da alluna masu hotunan Shugaba Muhammadu Buhari, mutanen sun yi kira ga gwamnatin Najeriya ta taimaka ta ceto musu 'yan uwansu.


Sun ce suna cikin matukar fargaba da rashin kwanciyar hankali watanni hudu bayan sace 'yan uwansu nasu.




Daya daga cikin masu zanga-zangar ya shaida wa BBC cewa ya je wajen ne saboda wata kanwarsa da ke cikin wadanda aka sace, wadda yanzu haka 'ya'yanta biyar ke cikin mawuyacin hali.


Ya ce wasu daga cikinsu sun hada kudi da zummar kai wa 'yan bindigar don sakin 'yan uwansu, amma gwamnati ta hana su.


Mutanen sun ce ba za su je ko ina daga wajen ba har sai sun ji daga bakin Shugaba Muhammadu Buhari da kansa.


'Bidiyon farfaganda ne'


Sai dai gwamnatin Najeriya ta ce bidiyon da ‘yan bindigar suka fitar wata farfaganda ce kawai.

Malam Garba Shehu, mai magana da yawun Shugaba Buhari, ya shaida wa BBC cewa dama ko ina a duniya ba bakon abu ba ne ga ‘yan ta’adda su fitar da fina-finai ko kalamai na firgitawa don su tsoratar da al’umma.


Ya ce "Suna yin hakan don su gigita gwamnatoci don su biya musu bukatunsu ko na siyasa ko kuma a biya su wasu kudade, don haka mu wannan abu ba sabo ba ne a wajenmu kuma watakila ba shi ne na karshe da za a gani ba.”


Malam Garba Shehu ya ce a baya an taba yin haka don sun gabatar da wata bukata da aka yi yarjejeniya da wakili da ke tsakani inda aka amince za su saki yara da mata 32, an biya musu bukatar, to amma daga karshe 11 suka saki.


Mai magana da yawun shugaban na Najeriya ya ce "Ko shakka babu duk dan uwa ko iyalin wadannan fasinjoji gaskiya suna cikin wani hali kuma babu abin da za a yi a dadada musu illa a dawo musu da dan uwa ko ‘yar uwarsu.”


Ya ce a gaskiya gwamnati na da wannan kyakkyawar fahimta, to amma batun cewa gwamnati ta gaza a bangarn jami’an tsaro ba bus hi.

Malam Garba Shehu ya ce "Shugaba Muhammadu Buhari kusan ya gabatar da duk wasu bukatu ga jami’an tsaro don suyi aiki.”

Ya ce "Ni ban isa na fadi cewa ga randa za a kubutar da fasinjojin nan ba, to amma ina so na tabbatar da cewa ‘yan Najeriya su zama cikin shiri don akwai matakai da zasu biyo baya.”

A cewarsa abin da jami’an tsaro ke nema shi ne kawai a ba su goyon baya.

Wadannan kalamai ko martini na gwamnatin Najeriyar na zuwa ne bayan 'yan bindigar da suka sace gomman fasinjojin jirgin kasan nan na Abuja zuwa Kaduna, tun ranar 28 ga watan Maris din da ya gabata, sun sake fitar da wani sabon hoton bidiyo da ke nuna mutanen da ake garkuwa da su cikin mummunan yanayi.

A cikin bidiyon mai tsawon kusan minti goma sha daya, an ga 'yan bindigar na lakadawa fasinjojin maza dukan tsiya da ita ce.

6 views0 comments
bottom of page