top of page
  • Writer's pictureArtv News

Dan majalisar tarayya ya raba takardun dauki a gwamnatin tarayya ga matasan mazabarsa guda takwas

Daga Abubakar Ahmad


Dan majalisar tarayya mai wakiltar yankin karamar hukumar Nassarawa, Alhaji Nassir Ali Ahmed, ya mika takardun daukar aiki da ya samawa matasan yankin su takwas a hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya daban-daban.


Da yake gabatar da jawabi a yayin wani kwarkwaryan bikin mika takardun wanda aka gudanar a ofishin yakin neman zabensa dake cikin kwaryar birnin Kano, Nassir Ali yace wannan yunkurin wani bangare ne na kudirorinsa da yake aiwatarwa tun lokacin da aka fara zabarsa domin wakiltar al’ummar yankinDan majalisar tarayyar wanda a cikin wannan makon ne aka sake zabarsa a karo na hudu domin ya tsayawa jam’iyyarsa ta APC takarar majalisar tarayya, ya ce ba zai taba gajiyawa ba wajen ci gaba da samawa matasan yankin ayyukan yi da nufin rabasu da zaman kasha wando

Yace tun lokacin da aka fara zabarsa don wakiltar yankin, ya samawa daruruwan matasa aikin yi, ya gina ajujuwaa makarantun masu yawa ya samar da rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana da masu amfani da wutar lantarki ya samar da asibitoci tare da daga darajar wasu da dai sauransu


Dangane da samar da tituna kuwa, Dan majalisar yace tuni aka fara aikin a unguwar Nasarawa sannan za a yi wani a Kawaji da Kaura Goje da Giginyu da ma sauran dukkanin mazabun dake yankin karamar Hukumar


Da ya juya kan batun bayar da tallafin kan sana’o’I kuwa, wakilin yankin a majalisar tarayya cewa yayi, sama da mutane dubu hamsin ne suka amfana daga irin wadannan shirye-shirye a tsawon wannan lokaci.


D

aga karshe ya kuma godewa gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa cikakken goyon baya da hadin kan da yake bashi a duk lokacin da bukatar hakan ta taso


Tunda farko da yake nasa jawabin, shugaban jam’iyyar APC na yankin karamar hukumar Nassarawa, Alhaji Salisu Ayo Gawuna, godewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi da tsohon shugaban karamar hukumar Alhaji Lamin Sani da sauran wadanda suka yi takarar majalisar jaha a yankin, bisa rawar da ya taka wajen cimma nasarar Nassir Ali Ahmed a yayin zaben fitar da gwani


A nasu jawabin daban-daban, matasan da dan majalisar ya samawa aikin, sun gode masa bisa aniyarsa ta inganta rayuwarsu da ta iyalansu da dukkanin ‘yan uwansu tare da yin alkawarin ba zasu ba shi kunya ba a dukkanin wuraren ayyukansu.


86 views0 comments
bottom of page