top of page
  • Writer's pictureArtv News

Dan Aminu Wali ya ci zaben fidda gwani na gwamna a jam'iyyar PDP


Dan tsohon Ministan Harkokin Waje Mohammed Sadiq Wali ya lashe zaben fidda gwanin takarar gwamna na jam'iyyar PDP a Kano. Wali ya samu kuri’u 455 inda ya doke Little na kusa da abokin hamayyarsa wanda ya zo na biyu da kuri’u 333. Politcs Disgest ta rawaito cewa an gudanar da zaben ne a Sani Abacha Youth Centre dake kan titin Madobi a Kano. Tsohon shugaban ma'aikatan Kwankwaso Dr Yunusa Adamu Dangwani ya samu kuri'u 276, Dr Yusuf Bello Dambatta wanda shi ne kwamishinan filaye da tsare-tsare na Kwankwaso ya samu kuri'u 182. Tsohon kwamishinan Ganduje Muaz Magaji ya samu kuri’u 25, Mustapha Bala Getso 20 da Muhuyi Magaji wanda ya samu kuri’u 25. A baya Magaji ya janye daga takarar gwamna domin neman kujerar Sanatan Kano ta Arewa ‘Yan takara shida ne suka fafata a zaben fidda gwani yayin da sauran ’yan takarar biyu Jafar Sani Bello da Muhammad Abacha suka shiga zaben fidda gwani da bangaren Sagagi na jam’iyyar ya gudanar. Shugaban kwamitin zaben Cif Bunmi Adu ya bayyana Wali da mafi yawan kuri’u a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani.

208 views0 comments
bottom of page