top of page
  • Writer's pictureArtv News

Dalibai 29,000 muka biya wa kudin NECO a bana — Gwamnatin Kano

Gwamnatin Jijhar Kano ta musanta rahotannin da ke cewa an hana daliban Jihar zana jarabawar kammala sakandare ta NECO ta shekarar 2022, bisa tarin bashin da Hukumar ke bin ta.Rahotanni da dama na nuna hukumar ta NECO ta ce ba za ta bar daliban su zauna jarabawar da aka fara gudanar da ita ranar Litinin ba, har sai gwamnatin ta biya ta ko da wani kaso ne daga bashin.


To sai dai Kwamishinan Yada Labaran Jihar, Malam Muhammad Garba, ya sanar da Aminiya a ranar Litinin cewa, “Ikirarin bin gwamnatin bashin har na Naira biliyan daya da rabi shifcin gizo ne kawai, domin kuwa tuni hukumar ta amince da tsarin da gwamnatin ta bijiro mata da shi na biyan kudin a hankali, na jarabawar daliban sama da 29,000 da ta dauki nauyi.


“Abin da ke faruwa shi ne yau [Litinin] ranar jarabawar gwaji ce da malamai a fadin kasar nan ke fitar da hanyoyin da za su gudanar da jarabawar gwaje-gwaje a aikace, kuma abu ne da sati guda ake kawashewa ana yi, kafin a je ga ainihin jarabawar,” inji shi.


“Kan batun bashi kuma, fiye da shekara biyar kenan NECO na bin mu bashin Naira miliyan 537, bisa yarjejeniyar cewa za mu dinga biyanta a hankali, kuma ya zuwa yanzu mun biya kusan miliyan 200 daga ciki, sannan kudin jarabawar bana ya kai wajen Naira miliyan 500 da rabi, amma abin da muka yi yarjejeniya shi ne za mu biya kudin bayan an kammala jarabawar, kafin fitowar sakamakonta”.


Muhammad Garba ya kuma ce jimillar kudin da ake bin gwamnatin idan an hada shi da na yanzu shi ne Naira miliyan 800, kuma tuni ma gwamnatin ta ba da sahalewar biyan Naira miliyan 300 daga ciki.


Kazalika ya ce gwamnatin ta Kano a jajirce ta ke wajen ganin an biya wadannan kudi cikin gaggawa, tare da bayyana cewa bashin da ake bin ta a halin yanzu na kudin jarabawar dalibai sama da 29,000 ne kawai, da gwamnati ta dauki nauyi.


Ya kuma ce “Gwamnati ta kuduri aniyar biyan dalibai 15,313 da suka samu credit tara a jarabawar qualifying ta makarantun sakandare da ta yi a 2021, wadanda suka hada da dalibai 1,018 da ke da bukata ta musamman, sai wasu 7,300 na shirinta musamman na gwamnatin da ya shafi ilimin ‘ya ‘ya mata, sai kuma Kananan Hukumomi da suka biyawa dalibai 5,400.
18 views0 comments
bottom of page