top of page

DCP Abba Kyari: Abin da ke faruwa da ɗan sandan izina ce ga sauran 'yan sanda – CP Mohammed Wakili

Updated: Aug 3, 2021

Tun bayan da hukumomi suka ɗauki matakin dakatar da DCP Abba Kyari daga aikin ɗan sanda bisa zargin karɓar cin hanci 'yan Najeriya ke tofa albarkacin bakinsu, ciki har da tsofaffin jami'an rundunar





Tsohon Kwamishinan 'Yan Sanda CP Mohammed Wakili ya faɗa wa BBC cewa halin da ofisan ya tsinci kansa "ya kamata ya faɗakar da 'yan baya su san cewa akwai gobe ta duniya kuma akwai gobe ta lahira".

Kafin yanzu, abu ne sananne cewa ɗan sanda Abba Kyari mai muƙamin Mataimakin Kwamishinan 'Yan Sanda (DCP) kuma shugaban tawagar tattara bayanan sirri ta Police Intelligence Response Team (IRT) na shan yabo kan yadda yake yaƙi da gawurtattun 'yan fashi a Najeriya, har ma ake yi masa laƙabi da "ɗan sanda na musamman".

Abba Kyari na da mabiya fiye da 445,000 a dandalin Facebook da kuma wasu 78,000 a Instagram, inda ya saba bayyana kusan dukkan ayyukansa - na gida da na ofis.


3 views0 comments
bottom of page