top of page

Gwamnatin Najeriya ta karɓi rigakafi korona miliyan huɗu daga Amurka

Updated: Aug 3, 2021

Gwamnatin Najeriya ta karɓi rigakafin korona miliyan hudu samfurin Moderna daga gwamnatin Biden na Amurka



An bada allurar ne karkashin shirin Covax, wanda aka kirkira domin tabbatar da tsarin raraba rigakafin cikin adalci a duniya.

Alluran sun iso Najeriya ne da misalin karfe 2:15am na ranar Lahadi a Abuja

Shugaban Amurka, Joe Biden a watan Mayu ya alkawarta cewa kasarsa za ta bada tallafin rigakafi miliyan 80 ga ƙasashen duniya domin kare matalauta da ƙasashe masu karamin karfi daga annobar.

Ana saran Afrika za su samu tallafin rigakafin miliyan 25, wanda tuni rukunni farko ya isa ƙasashen Burkina Faso da Djibouti da Ethiopia.




2 views0 comments
bottom of page